Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An cimma matsayar neman yiwa kashi 70 bisa dari na mutanen Afrikan riga-kafin ne a yayin taron kolin duniya game da annobar korona a gefen taron kolin MDD a wannan mako.
Ana cigaba da shigar da riga-kafin zuwa kasashen Afrika karkashin shirin samarwa da rarraba riga-kafin na COVAX, inda a makon jiya an kai allurai miliyan 4 zuwa nahiyar.
To sai dai kuma, har yanzu kashi uku kacal aka samar na riga-kafin da kasashe masu arziki suka yi alkawarin samarwa Afrika zuwa karshen shekarar 2021.
Daraktan hukumar WHO a shiyyar Afrika, Dr. Matshidiso Moeti, ta ce, ya kamata a tabbatar da wannan aniya a aikace maimakon kalaman fatar baki, sannan kasashen Afrika suna bukatar a fayyace takamammun ranakun shigar musu da riga-kafin domin su samu damar kimtsaya yadda ya kamata.
342/